Coronavirus ta tashi hankalin duniya | Zamantakewa | DW | 26.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Coronavirus ta tashi hankalin duniya

Al'ummar duniya na ci gaba da zama cikin firgici dangane da annobar cutar Coronavirus, duk da cewa ana warkewa.

Taiwan Taipei | Übung gegen Ausbreitung des Coronavirus (picture alliance/AP Images)

Har yanzu ana laluben maganin Coronavirus

Da fari dai cutar ta Coronavirus ko kuma COVID-19, ta bulla ne a kasar Chaina, kafin daga bisani sannu a hankali ta mamaye duniya baki daya. An yi gargadin cewa idan ba a dauki matakan kariya cikin gaggawa ba, cutar za ta yi gagarumar illa a duniya baki daya, ganin cewa har kawo yanzu ba ta da magani.

Wanna dai ya sanya firgici cikin zukatan al'umma, musamman a kasashe masu tasowa, da suke fama da dinbim talauci da halin rashin tabbas musamman a bangaren kiwon lafiya. Kasashen Afirka na daga cikin kasashen da ke fama da talauci da matsala a fannin kula da lafiyar al'umma, kuma kawo yanzu kasashe kalilan ne cutar ba ta isa ba a nahiyar.

Kawo yanzu dai cutar ta halaka mutane sama da dubu 22 a fadin duniya baki daya, yayin da wasu dubbai ke kwance a asibitoci suna fama, baya ga wasu masu tarin yawa da suka warke daga cutar.

DW.COM