Coronavirus ta janyo faduwar hannun jari | Labarai | DW | 21.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Coronavirus ta janyo faduwar hannun jari

Fargabar yaduwar cutar Coronavirus ta janyo faduwar hannayen jari a kasuwannin duniya a yayin da ake ci gaba da samun karuwar wadanda suka kamu da cutar a kasashen Labanan da Iran da kuma Italiya.

Kasuwar hannayen jari a kasashen duniya dabam-dabam musamman masu karfin tattalin arziki ta fadi a sakamakon fargabar yaduwar annobar Coronavirus da ta samo asali daga kasar Chaina.Farashi a kasuwannin kasashen Asiya da Amurka sun yi kasa sosai a wannan Juma’a, lamarin da ya kara tabbatar da fargabar da manyan kamfanoni suka baiyana na nakassun da cutar za ta iya yi wa tattalin arzikin duniya, a sakamakon yawan dogaro da ake yi da hajjojin Chaina, masana tattalin arziki sun nemi a sake lale.

Mutum fiye da dubu biyu da dari biyu ta Coronavirus ta hallaka baya ga wasu kimanin dubu saba'in da biyar da bincike ya nuna na dauke da cutar yanzu haka a Chaina. A yayin da aka samu karuwar masu dauke da cutar a kasashen Iran da Lebanon