1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus: Kamfanoni 5 da za su samar da maganin riga-kafi

Ramatu Garba Baba
June 3, 2020

Amirka ta tantance sunayen wasu kamfanoni biyar da ake sa ran za su gudanar da aikin samar da maganin riga-kafin cutar Coronavirus da yanzu haka kasashen duniya ke fadi-tashin ganin an dakile.

https://p.dw.com/p/3dDSy
Remdesivir antivirales Medikament in Erprobung
Hoto: picture-alliance/AP/Gilead Sciences

Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta fidda sunayen wasu kamfanoni biyar da ake son su gudanar da aikin samar da riga-kafin cutar Coronavirus, cikin kamfanonin akwai shahararren kamfanin hada magunguna na Pfizer da nan na Johnson and Johnson da da kuma jami'ar Oxford sauran sun hada da AstraZeneca da Merck & Co. A can baya, Hukumar Lafiya ta Duniya ta sha fadin cewa, maganin riga-kafin zai taka muhinmiyar rawa wurin bayar da kariya tare da kula da masu cutar idan sun kamu da ita.

Firaiminista Giuseppe Conte na Italiya ya ce kasar za ta ci gajiyar shirin Kungiyar Tarayyar Turai na tallafin Yuro biliyan ashirin don taimaka wa kasar da ta fuskanci ta'asa daga cutar Coroanvirus farfadowa, Conte ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a wannan Laraba.

A kasar Venezuela, Shugaban Nicholas Maduro da madugun adawa Juan Guiddo sun amince su ajiye sabanin siyasa a gefe don yin aikin tare a wani mataki na ceto kasar da ke fuskantar barazana daga annobar Coronavirus.

A kasar Senegal kuwa, an kona motoci 'yan sanda da motar daukar majinyata a yayin da rikici ya barke a garin Touba mai tazarar kilomita dari biyu daga Dakar babban birnin kasar, rikicin ya biyo bayan bijirewa dokar gwamnati na hana fita a matakan hana yaduwar cutar mai kama numfashi.