1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar corona na kara yin kamari a yankin Latin Amirka

Abdourahamane Hassane
May 20, 2020

Annobar coronavirus na ci gaba da yin mummunar barna a yankin Latin Amirka a daidai lokacin da a nahiyar Turai aka soma samun saukin cutar.

https://p.dw.com/p/3cXtx
Brasilien | Coronavirus
Hoto: Reuters/R. Patrasso

A karon farko kasar Brazil, mutane dubu sun mutu a cikin sa'oi 24 yayin da a Chile a rana daya aka samu sama da mutum dubu uku da suka kamu da cutar. Hakan na zuwa ne sa'ilin da Amirka ke zargin hukumar lafiya ta duniya WHO da nuna sakaci wajen kula da annobar ta corona. Yanzu haka dai hukumar lafiyar ta duniya ta amince da a gudanar da bincike a game da zargin da ake yi ma ta na nuna gazawa.