1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafin yakar COVID-19 ga Afirka

May 6, 2020

Yayin da ake fama da annobar coronavirus a kasashen duniya, wani abu da ke daukar hankali shi ne yadda gwamnatocin kasashen Afirka ke samun tallafin kudi daga kungiyoyi da daidaikun jama'a.

https://p.dw.com/p/3brkm
Nigeria Abuja | Coronavirus | Jack Ma Hilfsgüter
Tallafin kudi da kayan aiki ga AfirkaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Najeriya na daga cikin kasashen Afirka da suka samu irin wannan tallafi, inda tun farkon bullar cutar ta COVID-19, aka bayar da labarin samun gudummawa daga kamfanoni da kuma wasu kamfanoni da 'yan kasuwar kasar. Daga cikin wadanda suka bayar da gudunmawar har da hamshakin dan kasuwar Afirka Aliko Dangote da Abdul Samad Isyaku Rabiu shugaban rukunin kamfanonin BUA. Jamus na daga cikin kasashen da suka aike tallafi ga kwamitin yaki da cutar coronavirus a Najeriyar wato NDCD, tallafi na sama da Euro miliyan biyar. 

Tallafin kungiyoyi

Mako guda gabanin kyautar ta kasar Jamus, Najeriya ta samu tallafin sama da Euro miliyan daya daga Majalisar Dinkin Duniya. Gidauniyar Clara-Lionel ta mawakiya Rihanna ta yi alkawarin bayar da dalar Amirka miliyan biyar ga kasar Malawi. Haka ma Bankin Duniya da Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF, sun yi alkawarin yafe basussukan da suke bin kasashe 19 matalauta a nahiyar Afirka. 

Hamzat Lawal, Gründer von CODE in Nigeria
Hamzat Lawal wand ya kafa CODE a NajeriyaHoto: K. Gänsler

Wasu matasa sun kafa kungiyar da suka yi wa lak'abi abi kadin kudin tallafin na corona, wato #FollowCovid19Money. Guda daga cikin irin wadanna matasa shi ne Hamzat Lawal wanda ya kafa kungiyar Connected Development a Najeriya da kuma kungiyar nan ta Follow the Money, wacce ke bin diddigin yadda aka ba da kudin tallafi ga gwamnatoci.

Kasuwanci da kudin tallafi?

Yayin da kasashen Afirka ke cewa suna godiya da tallafin da suke samu, kuma suna iya kokarinsu na yin amfani da tallafin da suke samu a yaki da cututtuka dangin COVID-19, masu yaki da cin hanci na ganin cewa tamakar dai kawai kasuwa ce ta bude ga wasu daga cikin jami'an gwamnatocin nahiyar.