1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Corona ta kama dubban likitoci a Ghana

Gazali Abdou Tasawa MAB
July 17, 2020

Wasu alkalumman kididdiga da hukumomin kiwon lafiya a kasar Ghana suka fitar sun nunar da cewa ma'aikatan kiwon lafiya dubu biyu da 65 ne suka harbu da kwayoyin cutar Corona tun bayan bullarta a kasar.

https://p.dw.com/p/3fVt2
Ghana Tamale | Coronavirus | SDA-Krankenhaus
Hoto: DW/M. Suuk

Wasu alkalumman kididdiga da hukumomin kiwon lafiya a kasar Ghana suka fitar sun nunar da cewa ma'aikatan kiwon lafiya dubu biyu da 65 ne suka harbu da kwayoyin cutar Corona tun bayan bullarta a kasar.  Babban daraktan ma'aikatar lafiya na kasar wato Patrick Kumah-Aboagye ne ya sanar da hakan inda amma ya ce ma'aikatan kiwon lafiya shida ne kadai suka mutu daga cikin wadanda suka kamu da cutar.

A wannan Jumma'a dai masu dauke da cutar ta Corona, 19 ne suka rasu a kasar ta Ghana daga cikin mutane dubu 26 da 125 da suka kamu da ita. Kasar Ghana dai ta kasance daya daga cikin kasashen Afirka na Kudu ga Sahara da suka fi yin gwajin cutar ta Covid-19 tun bayan bullar annobar.  Sai dai duk da haka kungiyar kwadago ta ma'aikatan kiwon lafiyar kasar ta yi korafi kan rashin wadatattun kayan kariya ga liktoci da ma sauran al'umma.