Corona: Ayyukan Ista da azumin Ramadana | Siyasa | DW | 10.04.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Corona: Ayyukan Ista da azumin Ramadana

A bana bukukuwa da ayyuka na addini kamar Ista da azumin watan Ramadana sun zo ne a lokacin da duniya ke fama da annobar Coronavirus.

 Shin ya yi mabiya addinai dabam-dabam ke tafiyar da ayyukansu na ibada a wannan lokaci kasancewa an haramta haduwar mutane da yawa a wuri don yin ibada ko cin abinci ko biki?.

An dai hana haduwa ta ibada a majami'u da masallatai amma duk da haka babbar kofar shiga majami'ar Holy Ghost ko Ruhi mai tsarki ta Katholika da ke birnin Berlin na tarayyar Jamus, ta kasance a bude, domin a wannan lokaci na Corona coci na zama wani wurin samun nitsuwa ga mabiya da ke zuwa yin addu'o'i. Sai dai dab da shiga cocin akwai bayanai da nuna wa mabiya yadda za su zauna gida su yi ibada su kuma gudanar da bikin Ista. Haka yake a shafin intanet na coci da ma sauran majami'u a Jamus. Hakazlika limamin cocin Gerald Tanye yana gabatar da wa'azi ta shafin Youtube:

Ya ce: "Ya ku 'yan uwa mabiya ina yi muku marhabin da wannan lokaci. Ina fata kuna lafiya. Muna cikin wani lokaci mawuyaci da muke wa junanmu tambaya yadda za mu ci gaba da aikinmu har zuwa lokacin da abubuwa za su lafa."#

Da yawa daga cikin majami'un na amfani da intanet da kafafan talabijin wajen gabatar da sajada kai tsaye ga mabiya. Sai dai a addinin Muslunci bai kamata a samu shamaki tsakanin liman da mamu a lokacin salla kamar Jumma'a ba. Saboda haka babu damar gabatar da limancin ta intanet ko talabijin, mamu kuma su bi. A dalilin haka masalatai za su ci gaba da zama a rufe babu sallar jam'i a cikinsu.

Sai dai ba ya ga sallar su ma Musulmin suna gabatar da wa'azi da fadakarwa ta addini a intanet da sauran kafafan sada zumunta na zamani a cewar Odette Yilmaz shugabar kungiyar Musulmi masu sassaucin ra'ayi a Jamus.

#Ta ce: "Muna gabatar da wa'azi ta Youtube, muna amfani da wannan dama muna sanar da jama'a halin da ake ciki muna kuma kwantar musu da hankali. Yanzu a nan muka mayar da hankali kasancewa babu haduwa da juna ido da ido."#

Ko yaya maganar azumin watan Ramadana da ake kyautata zai fara a ranar 23 ga watan nan na Afrilu daidai lokacin da haramcin haduwar mutane da yawa waje daya ke aiki don dakile yaduwar Corona?. Ko da yake Yilmaz ta ce ko da yake babu cikakken bayani a addinance da tilasta haduwar mutane waje daya don yin bude baki yadda aka saba bisa al'ada, amma ta fi damuwa da yadda matakin hanin zai shafi rayuwa da zamantakewar al'umma.

Tun a tsakiya wannan makon dai babbar majalisar maluman ta jami'ar Azhar da ke Masar, sun ce ba za a iya ajiye azumi saboda Corona ba. Suka ce babu wata hujja a likitance da za ta sanya musulmi shan ruwa don rigakafin kamuwa da cutar corona face dama mutum na fama da wasu cutattukan na dabam ba.

A tsakiyar watan Maris ma kotun kolin Isra'ila ta yi watsi da kiran da a dakatar da muhimmin bikin Yahudawa na Pessach da ya kamata a yi daga 8 ga watan nan na Afrilu zuwa 16 ga wata. Sai dai saboda saboda Corona wuraren ibada a Birnin Kudus sun kasance wayam a wannan Ista, lokacin da ya kamata birnin ya sami baki daga ko ina cikin duniya.