1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Commonweath ta bayyana sabon jagora

April 20, 2018

Kungiyar kasashe renon Ingila wato Commonwealth ta amince cewar Yerima Charles zai gaji Sarauniyar Ingila a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar a nan gaba.

https://p.dw.com/p/2wQRv
Schloss Windsor Commonwealth Gipfel
Zaman da ya amince da sabon jagoran kungiyar Commonwealtha a IngilaHoto: Getty Images/AFP/H. Nicholls

Shugabannin kasashe 53 renon Ingila wato Commonwealth sun amince cewar Yerima Charles ya gaji Sarauniyar Ingilar wato Sarauniya Izabes a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar nan gaba. Shugabannin sun amince da hakan ne a wani zama da suka yi wajen birnin London a wannan Juma'a, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kungiyar da kuma makomarta na gaba. A jiya Alhamis ne dai sarauniyar ta Ingila ta ce tana son dan nata Yerima Charles ya karbi ragamar kungiyar daga hannunta.

A jawabin da ta yi a zaman na yau, Firaministar Birtaniya Theresa May, ta ce shugabannin na da batutuwa da za su yi nazarinsu da dama, dangane da makomar kungiyar ta commonwealth. Ba a dai yi karin bayani kan lokacin da Yerima Charles din zai kama ragamar wannan kungiya ba.