Clinton ta samu tambayoyi kafin muhawara | NRS-Import | DW | 01.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Clinton ta samu tambayoyi kafin muhawara

Kafar sadarwa ta Wikileaks ta kwarmato sakonnin da ke nuna cewar 'yar takara a zaben Amirka Hillary Clinton ta samu tambayoyi kafin muhawarar da ta yi da Donald Trump.

Wata badakala ta sake kunno kai a yakin neman zaben 'yar takara Hillary Clinton mako guda kafin a gudanar da zaben shugaban kasar Amirka. Wasu sakonni da kafar Wikileaks ta kwarmato sun jaddada zargin da dan takara Donald Trump ya yi ,na cewar abokiyar karawarsa Hillary Clinton ta samu tambayoyi tun kafin a gudanar da muhawara a tsakaninsu.

Wata mai sharhi kan harkokin siyasa a tashar CNN Donna Brazile ce ta tura wa darektan yakin neman zaben Clinton wadannan tambayoyi, kwana guda kafin muhawarar, inda ta bayyana suffar matar da zata yi wannan tambaya da tambayar ita kanta. Sannan daga bisani ta ce zata ci gaba da tura wa bangaren 'yar takarar Democrat Hillary Clinton tambayoyin da take samu.

Dama dai Donald Trump ya dade ya na korafin cewar Hillary Clinton na samun hadin kan wasu masu ruwa da tsaki a harkar shirya muhawara. Tuni dai Donna Brazile da ta tura da tambayoyin ta ajiye aiki a tashar talabijin ta CNN. Kafar ta wikileaks ta sato wadannan bayanai ne a shafin e-mial na daya daga cikin na hannun daman Hillary Clinton bisa tallafin injiniyoyin Rasha. Sai dai har yanzu jam'Iyyar Democrat ba tace uffan kan wannan batu ba.