Cisse Jagoran 'yan adawa a Mali ya rasu | Labarai | DW | 25.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Soumaila Cisse madugun adawa a Mali ya rasu

Cisse Jagoran 'yan adawa a Mali ya rasu

Cisse ya rasu watanni biyu bayan fita daga hannun 'yan tada kayar baya da suka yi garkuwa da shi a watan Maris, yayin gangamin yakin neman zabe a Timbuktu.

Makusantan marigayin sun tabbatar da mutuwarsa a birnin Paris na kasar Faransa, sai dai babu karin bayani kan hakikanin cutar da ta yi ajalinsa.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 71 a duniya, ya kuma taba rike mukamin ministan kudin kasar Mali.

Soumaila Cisse ya sha gwagarmayar siyasa tare da neman takarar shugabancin kasar Mali har sau biyu, yana cikin 'yan takarar da ake kyautata zaton za su yi tasiri a zaben kasar na shekarar 2022 idan sojoji suka kammala wa'adin mulkin rikon kwarya da aka kafa bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita a watan Agusta 2020.