Cinkoson gidajen kaso na kasar Faransa | Labarai | DW | 19.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cinkoson gidajen kaso na kasar Faransa

Yayin wani zama na kwamitin kare hakin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya, kasashe da dama na duniya sun yi kira ga kasar Faransa kan cewa ta inganta tsarinta na tafiyar da gidajen kason kasarta.

Sainte-Anne Gefängnis in Südfrankreich (AP)

Gidan kaso na Sainte-Anne da ke Kudancin Faransa

Wannan kira na daga cikin shawarwari har guda 300 da kwamitin ya bai wa kasar ta Faransa na ganin ta inganta tsarin nata na kula da gidajen kasonta da suke fama da tarin matsaloli na cinkoson jama'a.

Wannan mataki na daga cikin tsarin kwamitin, inda duk bayan shekaru hudu ake zabar wata kasa domin duba tsarinta na kare hakin bil-Adama.

Kasashen kuma sun yi kira ga kasar ta Faransa da ta tabbatar cewa dokokinta da take amfani da su na yaki da ta'addanci, dokoki ne da suka dace da dokokin kasa da kasa har ma abin da ya shafi 'yan gudun hijira masu karancin shekaru.