Cikas ga kokarin sulhunta rikicin Masar | Labarai | DW | 12.12.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cikas ga kokarin sulhunta rikicin Masar

Karancin mahalarta taron sulhu a Masar ya tilastawa sojoji jinkirta gudanar dashi.

Wani kakakin rundunar sojin kasar Masar ya sanar da dage fara gudanar da taron neman maslaha ga rikicin siyasar kasar, wanda a da hukumomin suka tsara yi a wannan Larabar da nufin shawo kan takaddamar da ta dabaibaye batun jefa kuri'ar raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar. Dage taron dai ya zo ne sakamakon karancin wadanda aka turawa goron gayyata, duk kuwa da tabbacin da jam'iyyar 'yan uwa Musulmi da kuma kungiyoyin adawa suka yi na cewar za su halarta. Sai dai kuma babu wata alamar da ke nuna lokacin da za'a sake komawa ga taron. Kasar Masar dai ta sake fadawa cikin rudanin siyasa tun bayan karin ikon da shugaban kasar ya baiwa kansa, wanda daga baya kuma ya janye sakamakon jerin zanga-zangar nuna goyon baya da na adawa da matakin, da kuma takaddama akan daftarin tsarin mulkin kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas

 • Kwanan wata 12.12.2012
 • Rahotanni masu dangantaka Masar
 • Muhimman kalmomi Masar
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/170Uu
 • Kwanan wata 12.12.2012
 • Rahotanni masu dangantaka Masar
 • Muhimman kalmomi Masar
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/170Uu