1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gudanar da zanga-zangar sauyi a Aljeriya

Gazali Abdou Tasawa MNA
April 19, 2019

A kasar Aljeriya masu zanga-zangar neman sauyi sun sake fantsama a saman titunan biranen kasar da dama domin nuna rashin amincewarsu da gwamnatin rikon karya da sojoji suka kafa.

https://p.dw.com/p/3H6PU
Algerien, Freitagsdemo
Hoto: picture alliance/dpa

A kasar Aljeriya masu zanga-zangar neman sauyi sun sake fantsama a saman titunan biranen kasar da dama domin nuna rashin amincewarsu da gwamnatin rikon karya da sojoji suka kafa bayan murabus din tsohon shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika.

Ko da shike babu wasu alkalumma na gwamnati ko na masu zanga-zangar kan adadin mutanen da suka fito a wannan Juma'a da ke zama karo na tara, to amma masu aiko da rahotanni sun ce jama'a sun fito dafifi a babban birnin kasar Algiers da kuma a manyan garuruwan Oran da Annaba da Constantine kai har ma a wasu matsakaitan biranen kasar irin su Setif da El-Oued ta yankin Sahara. 

Masu zanga-zangar dai sun sha alwashin ci gaba da fitowa har zuwa ranar da sabon shugaban mulkin sojan rikon kwarya na kasar Abdelkader Bensalah da kuma Firaminista Noureddine Bedoui suka mika mulki ga farar hula. 

Wannan zanga-zanga na ci gaba ne kwanaki kalilan bayan da Tayeb Belaiz shugaban kotun tsarin mulkin kasar ta Aljeriya daya daga cikin mukarraban Bouteflika da masu neman sauyin saku tsana ya yi murabus daga kan mukaminsa.