Ci gaban zanga-zangar adawa da Trump a Amurka | Labarai | DW | 11.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban zanga-zangar adawa da Trump a Amurka

An shiga dare na biyu a zanga-zangar nuna adawa da nasarar Donald Trump a matsayin shugaban kasa, a wasu biranen kasar Amurka.

A biranen Washington da Baltimore da Philadelphia da New York, masu gangami sun mamaye tituna a wani mataki na nuna bacin ransu kan nasarar da Trump ya samu. Kazalika dubban masu boren ne suka yi cincirindo a Los Angeles da San Francisco da Oakland da California da Portland da Oregon.

Duk da cewar yawancin zanga-zangar na gudana ne cikin lumana, ana gudanar da su ne a kan tituna wanda ke haifar da cikas ga harkokin sufuri da hada-hadar yau da kullum. Rahotanni na nuni da cewar gangamin na ranar Alhamis bai kai wadanda aka yi ranar Laraba ba. A birnin Washington, mutane wajen 100 ne suka yi tattaki zuwa fadar gwamnati ta white inda shugaba Barack Obama ya yi ganawarsa ta farko da mai gadon kujerarsa Donald Trump.