1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban tashe-tashen hankula a Benghazi

October 9, 2014

Kusan kullun ana fuskantar rikici tsakanin mayaka masu rajin girka shari'ar Muslunci a kasar ta Libiya, da kuma sojoji masu biyayya ga gwamnatin kasar.

https://p.dw.com/p/1DSpG
Hoto: Reuters

Rahotanni daga kasar Libiya na cewa mutane 17 suka rasu cikin su sojoji 14 a cikin kwanaki uku, sakamakon fadan da ke wakana a kewayan filin jiragen saman birnin Benghazi, tsakanin mayaka masu rajin kafa shari'ar Muslunci, da kuma sojojin da ke biyayya ga gwamnatin kasar.

Wasu majiyoyi na jami'an tsaro da gidajen asibiti suka tabbatar da wannan adadi, inda a cewar majiyar asibitocin, rikicin ya yi sanadiyar mutuwar Salim Nabbous, wanda yake daya daga cikin kwamandojin Majalisar Chura ta 'yan juyin-juya halin Benghazi, majalisar da ta kumshi mayakan jihadi na Ansar Ashari'a.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo