Ci gaba da zubar da jini a Siriya
December 12, 2012Wasu abubuwan da suka tarwatse - ciki harda bam da aka dasa cikin wata mota a farfajiyar ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Siriya sun janyo mutuwar akalla mutane bakwai, yayin da wasu 50 kuma suka sami rauni. Jami'an tsaron Siriyar da suka sana da hakan a wannan Larabar (12.12.12), suka ce ministan kula da harkokin cikin gidan Siriyar Mohammad al-Shaar, ya tsira daga harin - ba tare da jin rauni ba.
Tunda faro dai kanfanin dilancin labaran Siriya SANA ya ce bama-bamai ukku ne suka fashe a wajen ma'aikatar cikin gidan da ke birnin Damascus ta yankin kudu-maso-yammacin unguwar Kfar Sousa, daya daga ciki kuma a cikin wata mota ce.
A halin da ake ciki kuma kasashe 120 da ake yiwa lakabi da kawayn Siriya sun amince da kawancen 'yan adawar Siriya a matsayin sahihan wakilan al'ummar kasar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal