Ci gaba da tsaurara matakan tsaro a Brussels | Labarai | DW | 23.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da tsaurara matakan tsaro a Brussels

Hukumomin Belgiyam sun dauki matakin ci gaba da daukar tsauraran matakan tsaro a kwana na uku a birnin Brussels inda ake ci gaba da farautar mutanen da ake zargi da hannu a harin Paris

A kasar Belgiyam a yau aka shiga rana ta uku ta ci gaba da da daukar tsararan matakan tsaro a wani matakin na rigakafin hana abkuwar hare-haren ta'addanci da ake fargabar yiwuwar fuskanta a kasar.

Bayan da 'yan sanda suka share yinin jiya Lahadi suna gudanar da bincike ba tare da yin nasarar kame Salah Abdeslam wanda ake zargi da kitsa harin birnin Paris ba, hukumomin bincike na kasar ta Belgiyam sun bayyana a yau Litanin cewa kawo yanzu dai sun kama mutane 16 a binciken da suka gudanar a unguwal Molenbeek inda ake ci gaba da fuskantar barazana.

Thierry Weerts daya daga cikin hukumomin binciken ya shaida wa manema labarai a yau Litanin cewa a lokacin wani aikin bincike a Molenbeek,wata mota tun tunkaru 'yan sanda a guje wadanda su kuma suka buda mata wuta nan take. Motar ta yi nasarar tserewa ,amma an kamota a Brussels kuma an kama mutumnan da ke cikinta wanda ya ji rauni.

Ko a wannan Litanin dai tashoshin jiragen kasa dama makarantun boko tun daga na renon yara har zuwa jami'o'i na birnin na Brussels mai kunshe da mutane miliyon daya da dubu 200 za su ci gaba da kasancewa a rufe.