Ci gaba da kamen ′yan jarida a Turkiya | Labarai | DW | 10.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da kamen 'yan jarida a Turkiya

Hukumomin shari'ar Turkiyya sun ba da sammacin kamo wasu ma'aikatan kafofin yada labarai 35 da ake zargi da alaka da shafukan sada zumunta na Fetullah Güllen.

Hukumomin shari'ar kasar Turkiyya sun bada sammacin kamo wasu ma'aikatan kafofin yada labarai 35 a karkashin wani aikin bincike da suke kan alakar da ke da akwai tsakanin wasu kafofin yada labarai na kasar da shafukan sada zumunta na Fetullah Güllen shahararran malamin nan dan asalin kasar ta Turkiyya da ke zaman gudun hijira a Amirka da mahukuntan Turkiyyar ke zargi da kitsa juyin mulkin da ya ci tura a kasar a watan Yulin 2016. 

Kamfanin dillancin labaran gwamnati Turkiyyar na Anadolu ya ruwaito cewa tun da sanyin safiyar wannan Alhamis mahukuntan suka kama tara daga cikin mutanen wadanda ake zargi da kasancewa mambobin wata kungiyar 'yan ta'adda. 

Mahukuntan Turkiyyar na zargin mutanen da yin amfani da kafar aikewa da sakonni mai layar zana ta Bylock wacce ta kasance kafar da mutanen da suka kitsa juyin mulkin suka yi amfani da ita wajen musayar sakonni a tsakaninsu.