Ci gaba da gwabza fada a Yemen | Labarai | DW | 15.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da gwabza fada a Yemen

Mayakan sa kai na Yemen sun samu nasarar kwace tashar jiragen ruwa ta kudancin birnin Aden daga hannun 'yan tawayen Houthi.

Rikicin kasar Yemen

Rikicin kasar Yemen

Mayakan sa kan da ke goyon bayan gwamnatin Shugaba Abed Rabbo Mansur Hadi dai, sun samu wannan nasarar ne tare da goyon bayan dakarun kasar Saudiya. Rahotanni daga mazauna gundumar Mualla da ke daf da tashar jiragen ruwan na nunar da cewa mayakan sun kuma samu nasarar kwace iko da wannan gunduma wadda a baya ita ma ke karkashin ikon mayakan na Houthi. Tun dai cikin watan Maris din da ya gabata ne Saudiyan ta fara jagorantar kawayenta kasashen Larabawa wajen kai farmaki da yin ruwan bama-bamai a kan mayakan tawayen na Houthi da suke zargin Iran na mara musu baya, a abin da Saudiyan da kawayen nata suka kira da kokarin kare halastacciyar gwamnatin kasar.