Ci gaba da fafata fada a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 21.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da fafata fada a Sudan ta Kudu

'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun musanta ikirarin gwamnati na kwace garin Malakal

'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun musanta ikirarin gwamnatin kasar na sake kwato garin Malakal.

Garin na Malakal ya kasance karkashin gwamnati da 'yan tawaye cikin wata guda da aka shafe ana fafatawa tsakanin bangarorin. Rikicin ya samo asali lokacin da Shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnati.

Wani kiyasin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna dubban mutane sun hallaka, yayin da wasu kimanin rabin miliyan suka tsere daga gidajensu sakamakon rikicin na Sudan ta Kudu. Masu shiga tsakani na fata bangarorin da ke rikici da juna za su amince da shirin tsagaita wuta.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh