Christian Kaboré ya yi rantsuwar kama aiki | Labarai | DW | 29.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Christian Kaboré ya yi rantsuwar kama aiki

Sabon shugaban kasar Burkina Faso wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 29 ga watan Nuwamba da ya gabata, ya yi kira ga 'yan kasar da su canza tunaninsu.

Sabon shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré ya yi rantsuwar kama aiki da tsakiyar ranar wannan Talatar, tare da halartar shugabannin kasashe da dama na Afirka da suka hada da na Côte d'Ivoire, Mali, Nijar, Sénégal, da na Guinea.

Wannan biki ya kawo karshen mulkin rikon kwarya da aka gudanar bayan faduwar gwamnatin shugaba Blaise Compaore a karkashin shugaba Michel Kafando wanda ya ce hakan wata babbar nasara ce ga demokaradiyya da 'yancin al'umma.

Dan shekaru 58 da haihuwa, sabon shugaban kasar ta Burkina Faso ya yi kira ga 'yan kasar da su dukufa wajen sauya halayyarsu, domin a samu cimma nasarar bunkasa kasar tare da karfafa ma'aikatunta, da ci gaban demokaradiyya da 'yanci al'umma.