Chirac yayi adawa da gurfanar da Iran gaban komitin sulhu | Labarai | DW | 18.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chirac yayi adawa da gurfanar da Iran gaban komitin sulhu

Shugaba Jacques Chirac na Faransa yayi kira ga manyan kasashe masu fada aji da kada su gurfanar da Iran gaban komitin sulhun mdd adangane da shirin Nuclearnta,kuma babu dalilin da zasu jagoranci kaka mata takunkumi.sai dai a hiran da manema labaru sukayi dashi,shuganan na Faransa ,yayi kira ga Tehran data dakatar da bunkasa sinadran Uranium data cigaba dayi a halin yanzu.Shugaba Chirac ya jaddada bukatar yin mahawara,a matsayin hanya mafi sauki na warware kowace irin matsala data kunno kai.Shugaban hukumar kula da harkokin Nulear ta mdd Mohammad Elkbaradei a nashi bangare,yayi fatan cewa Iran da kasashen yammaci zasu koma teburin sulhu domin wasrware wannan takaddama.Elbaradei yayi wannan furuci ne a taron hukumar IAEA da aka kaddamar ayau litinin a birnin Vienna.

 • Kwanan wata 18.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu5R
 • Kwanan wata 18.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu5R