Chibok na neman ɗauki daga Majalisar Ɗinkin Duniya | Siyasa | DW | 04.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Chibok na neman ɗauki daga Majalisar Ɗinkin Duniya

Al'ummar Chibok da ke Najeriya sun yanke shawarar tinkarar Majalisar Ɗinkin Duniya, domin samun kariya daga hare-haren Boko Haram da ma ceto ‘yan matan da aka sace.

Al'ummar yankin Chibok da ke jihar Borno da suka yi taro ga 'yan jaridu a Abuja sun bayyana matuƙar bacin ransu a kan abin da suka kira kissan ƙare dangi da ake yi musu.

Saboda ci gaba da fuskanta kai masu hare-hare, duk kuwa da sanar da hukumomin tsaro wasiƙun gargaɗin da suke samu daga musu kai masu harin , lamarin da ya sa suka bayyana cewar dole ce ƙanwar na ƙi su tinkari Majalisar Ɗinkin Duniyar domin neman a kawo musu ɗauki.

Kusan hare-hare 15 aka kai a Chibok tun bayan sace 'yan matan 'yan makaranta su 200

Domin kuwa tun bayan sace ‘yan matan nan sama da ɗari biyu na makarantar sakandire ta Chibok an kai musu hare-hare 15 a ƙauyyuka 19 na yankin Chibok ɗin wanda ya yi dalilin kashe fiye da mutane 229 tare da raunata wasu 100.

To amma suna ganin a yanzu gwamnatin ta gaza ne suke neman tallafin Majalisar Ɗinkin Duniyar Dr Bitrus Pogu shi ne shugaban al'ummar Kibaki da ke ChiboK ɗin da ya yi wa 'yan jaridu ƙarin bayyani a kan matakin nasu.

‘' Mun yi ta ƙoƙari mun yi ta kuka cewar a taimaki ‘yan banga don sune suke aikin soja za su zauna ana ta kashe mutane su barsu ba wani taimako, ba'a yi ba to ina za mu je''

Abin jira a gani shi ne ko matakin tinkrar Majalisar Ɗinkin Duniyar zai iya yin tasiri wajen kawo ƙarshen kai hare-hare a kan ƙauyyukan da ke yankin na Chibok da ma sauran yankuna na jihar ta Borno a wannan yanayi na taɓarɓarewar rashin tsaro a Najeriyar.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto da kuma rahoton da Suleiman Babayo ya haɗa mana dangane da yadda jama'a ke kallon lamarin na Boko Haram A Najeriya

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin