1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Chaina ta nemi Isra'ila ta daina kashe fararen hula a Gaza

Mouhamadou Awal Balarabe
March 7, 2024

Ministan harkokin wajen Chaina Wang Yi ya yi kira ga Isra'ila da ta daina kai hare-hare kan fararen hula a yakin da take yi da Hamas a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4dGIY
Ministan harkokin wajen Rasha Wang Yi
Ministan harkokin wajen Rasha Wang YiHoto: Wang Zhao/AFP

A yayin da yake bayani ga manema labarai a birnin Beijing a bayan taron majalisar dokokin kasar, Wang Yi ya ce kamata ya yi kasashen duniya su goyi bayan matakan cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da samar da kasar Falasdinu mai cikakken iko.

Karin bayani: An yi gargadin illar yakin Gaza kan tattalin arzikin duniya

Ya ce: "Abin takaici ne kuma abin kunya ne a ce a wannan karni na 21, ba za a iya dakatar da wadannan kashe-kashen bil'adama ba. Bbabu dalilin da zai sa a ci gaba da wannan rikici, kuma babu hujjar ci gaba da kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba."

Karin bayani: Duniya na muradin kafa kasar Falasdinu

Wannan yaki da ma'aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana cewar ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 30,800, ya shiga wata na shida duk da kokarin da masu shiga tsakani ke yi don magance matsalar jin kai da ake fama da ita a yankin Falasdinawa. Hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke kaiwa ba tare da kama hannun yaro ba ya yi sanadiyar mutuwar mutane 83 cikin sa'o'i 24 na baya-bayannan.