1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Chaina da Amurka na takaddama kan mallakar kanfanin TikTok

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
March 14, 2024

Chaina ta mayar da martani bayan da majalisar wakilan Amurka ta kada kuri'ar amincewa da dokar tanadin tilasta wa dandalin TikTok sayar da kamfaninsa ga Amurka, ko kuma a toshe amfani da shi a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/4dVme
Kanfanin TikTok mallakin Chaina ne
Kanfanin TikTok mallakin Chaina neHoto: AFP/O. Douliery

'Yan majalisa 352 ne suka kada kuri'ar amincewa da kudurin toshe TikTok matukar ya ki sayar da kamfani ga Amurka, yayin da 65 suka nuna adawa da kudurin dokar. Kakain majalisar dokoki ya ce: "Masu goyon bayan kudurin sun samu nasar, kuma an amince da shi". Shi ko Dan Bishop daga North Carolina,cewa ya yi: "Bana amfani da TikTok, kuma a ganina babu wayewa sam wajen amfani da dandalin, wasu daga cikinmu na ta'ammali da shi, kuma sun shahara, ina kuma martaba ra'ayin Amurkawa miliyan 170 da suka zabi amfani da shi".

Karin bayani: Najeriya: Kamen 'yar TikTok a jihar Kano

Amurkawa fiye da miliyan 170 ne ke amfani da TikTok
Amurkawa fiye da miliyan 170 ne ke amfani da TikTokHoto: NICOLAS ASFOURI/AFP

Amurka ta ce wannan wani mataki ne kare harkokin tsaron kasarta daga duk wani kutse na makiya, da kuma kin amincewa da yadda kamfanin TikTok ke bin diddigin sirrin abokan huladarsa, kamar yadda wasu 'yan majalisar suka yi ikirari a zauren majalisar. Raja Krishnamoorthi daga Illinois, ya ce "Fatanmu shi ne TikTok ya ci gaba da aiki, amma ba karkashin jam'iyyar kwaminisanci ta China ba, sirrin dakarun sojinmu da jami'an gwamnati masu akidar neman jinsi na fadawa hannun wannan jam'iyya ta China, don haka dole a sayar da kamfanin".

Karin bayanEU ta shimfidawa TikTok wasu sabbin sharuddai: 

Shugaban masu rinjaye na majlisar dattijan Amurka Chuck Schumer
Shugaban masu rinjaye na majlisar dattijan Amurka Chuck SchumerHoto: Nathan Posner/Anadolu/picture alliance

A bangarensa, shugaban masu rinjaye na majlisar dattijan Amurka Chuck Schumer ya ce zai tuntubi shugabannin kwamitocin majalisar don jin ra'ayinsu a kan wannan doka, kafin amincewa da ita. Tuni da fadar mulkin kasar ta White House ta sanar da cewa shugaba Joe Biden ya shirya tsaf don rattaba hannu kan dokar bayan wata ganawar sirri da da ya yi da 'yan majalisar game da sha'anin tsaron Amurka. Amurkawa fiye da miliyan 170 ne dai ke amfani da TikTok.

Karin bayani: Amirka ta dakatar da manhajar TikTok da WeChat

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Chaina Wang Wenbin ya ce matakin majalisar ya saba da tsare-tsaren gudanar da kasuwancin kasa-da-kasa cikin adalci ga kowa da kowa a duniya.