Chadi za ta janye dakarunta daga Kungiyar MISCA | Labarai | DW | 03.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi za ta janye dakarunta daga Kungiyar MISCA

Kasar Chadi ta nuna kosawarta dangane da zargin bata sunan da ta ce ana yi wa sojojinta, inda ta dauki aniyar janye su daga Afirka ta Tsakiya.

A wannan Alhamis din ce, Chadi ta sanar da aniyar ta, na janye dukkan dakarunta da ke ayyukan kiyaye zaman lafiya a karkashin Kunygiyar Tarayyar Afirka ta Misca a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Kasar ta Chadi dai ta ce ta gaji da kalaman da ake yi a kullu yaumin, na bata wa dakarunta suna a wannan kasa, duk kuwa da irin jan kokarin da suke yi a fannin samar da zaman lafiya.

A kan haka ne bayan ta sanar da shugabar rikon kwaryar kasar ta Afirka ta Tsakiya, da kuma Tarayyar Afirka, sannan da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, kasar ta Chadi ta bayyana wannan aniya tata na janye dakarunta daga wannan kasa.

Daga cikin dakarun na Misca 6,000 dai, kasar Chadi na da yawan dakaru 850. Sai dai kuma ana ganin cewa dakaru 800 da kungiyar Tarayyar Turai ta amince ta turawa wannan kasa ba za su wadatas ba, a bukatun da ake da su na yawan dakaru a wannan kasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita Zainab Mohamed Abubakar