1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta samu sabon kundin tsarin mulki

Salissou Boukari MNA
March 28, 2018

Wani babban taro da 'yan kasar Chadi suka gudanar na tsawon kwanaki 10, ya ba da damar kaiwa ga kaddamar da sabon kundin tsarin mulki, wanda zai kasance mai ruwa daya.

https://p.dw.com/p/2v6Uf
Präsident Tschad - Idriss Déby Itno
Hoto: UImago/Xinhua/C. Yichen

Sai dai 'yan adawar kasar ta Chadi ba su halarci zaman taron ba, amma mafi yawan mahalarta taron sun aminta kan tsarin mulki mai ruwa daya, inda shugaban kasa ke da cikakken iko maimakon tsarin mulki mai ruwa biyu da ake da shi a kasar ta Chadi.

Wannan sabon kundin tsarin mulkin ya tanadi cewa shugaban kasa zai yi shekaru shida ne maimakon biyar a wa'adi daya na mulki, sannan yana iya neman wa'adin mulki na biyu, yayin da wa'adin mulkin 'yan majalisa zai kasance na shekaru biyar maimakon hudu.

Yayin da yake jawabi wajen rufe wannan taro, Shugaban kasar ta Chadi Idriss Debi Itno ya ce a nan gaba mata za su samu babbar dama wajen shiga cikin harkokin tafiyar da mulkin kasa, inda maimakon kaso da ake ba su, za su kasance kankankan da yawan da maza suke da shi a sassa dabam-dabam na madafun iko.