Chadi ta ayyana zaman makoki na kwanki uku
May 7, 2026
Talla
Jiragen kwale-kwale na tsaro da jami’ai da ke aikin sintiri a yankin, harin mayakan Boko Haram ya rutsa da su, a cewar wani jami'in soji da ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, inda ya kara da cewa an kashe janar-janar guda biyu.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin Chadi ta fitar, ta ayyana zaman makoki na kasa har zuwa ranar Asabar 9 ga watan Mayu domin girmama sojojin da wannan hari ya yi ajalinsu.
Shugaban kasar Janar Mahamat Idris Deby Itino ya sha alwashin ganin bayan 'yan ta'adda da suka addabi kasar.
Karin bayani: kasar Chadi ta shiga rudani bayan harin Boko Haram