1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chadi: Sojoji sun halaka madugun adawa Yaya Dillo

February 29, 2024

Hukumomin Chadi sun sanar da mutuwar dan adawa Yaya Dillo Djérou a harin da sojojin kasar suka kai wa hedikwatar jam'iyyarsa, watanni biyu gabanin gudanar da zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/4d2qU
Sojoji Chadi sun halaka madugun adawa Yaya Dillo
Sojoji Chadi sun halaka madugun adawa Yaya DilloHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Dama dai ana bayyana Yaya Dillo Djérou a matsayin babban abokin hamayyar shugaban gwamnatin mulkin sojan Chadi Janar Mahamat Idriss Déby Itno wanda ya dare kan karagar mulki bayan mutuwar mahaifinsa.

 A lokacin da yabayyana a gidan rediyo don yin cikakken bayani kan yanayin harin, ministan sadarwa Abderaman Koulamallah ya ba da rahoton mutuwar 'yan sanda hudu da mutuwar mutane uku a cikin 'yan jam'iyyar PSF.

Sanarwar mutuwar Mista Dillo ta zo ne kwana daya bayan tashe-tashen hankula a tsakiyar birnin N'Djamena, inda jami'an tsaro suka yi amfani da bindigogi tare da harba barkonon tsohuwa a kusa da hedkwatar jam'iyyar ta PSF, inda ya fake.

Karin bayani: Hari a Chadi ya hallaka mutane da dama

Gwamnati Ndjamena na zargin Yaya Dillo da kai hari a daren Laraba zuwa Alhamis a hedkwatar hukumar leken asiri ta ANSE, a matsayin ramuwar gayya kan kama dan jam'iyyarsa da aka yi. Wannan harin da Mista Dillo ya kai a cewar gwamnati ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.