Chadi: Sabuwar gwamnatin rikon kwarya | Siyasa | DW | 03.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Chadi: Sabuwar gwamnatin rikon kwarya

Shugaban majalisar sojojin gwamnatin rikon kwaryar kasar Chadi ya bayyana sunayen ministocin gwamnati, karkashin jagorancin Firaminista Pahimi Albert Paraclet.

Tschad | Mahamat Idriss Déby, Präsident des Übergangs-Militärrates (CMT)

Shugaban gwamnatin wucin-gadi ta soja a Chadi Mahamat Idriss Déby

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai ministocin tshuwar gwamnatin marigayi Idriss Deby da aka yi wa kisan gilla a ranar 19 ga watan Afrilun da ya gabata, inda kuma aka bayyana dansa da shima soja ne wato Mahamat Idriss Deby a matsayin wanda yake jagorantar gwamnatin wucin-gadi da za ta shirya zabe cikin watanni 18 masu zuwa. Haka kuma akwai jami'an sojoji masu yawa cikin sabuwar gwamnatin ta rikon kwarya.

Karin Bayani: Boren kin amincewa da gwamnatin Chadi

Koda yake akwai tsofaffin 'yan adawa da gwamnatin Idriss Deby Itno kamar Mahamat Ahmat Alhabbo a matsayin ministan Shari'a, sai dai madugun 'yan adawar Chadin Saleh Kebzabo bai samu shiga gwamnatin ba, amma an sa sunayen mutune biyu daga cikin jam'iyarsa. Mace daya tilo da ta tsaya takarar neman shugabancin kasar ta Chadi a zaben watan Afrilun da ya gabata, Madam Ladi Bayasinde ta samu matsayin ministan ilimi mai zurfi da bincike.

Chadi dai na zaman babbar kawa kana mai matukar muhimmanci ga kasar Faransa da ta yi mata mulkin mallaka da kuma nahiyar Turai a yankin Sahel, yankin da ke fama da barazana daga kungiyoyi masu dauke makamai da na 'yan tawaye da kuma na 'yana ta'adda da ke yin kisan ba gaira.