Chadi: Dan adawa Mahamat Adoum ya shiga hannu | Labarai | DW | 06.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi: Dan adawa Mahamat Adoum ya shiga hannu

Hukumomin Chadi sun kame Mahamat Adoum, shugaban wata jam'iyyar adawa, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gidan yari na Moundou da ke kudancin kasar inda ake tsare da wani dan adawa Laokein Medar.

Tschad Proteste Zivillgesellschaftsorganisationen und Opposition (DW/D. Blaise)

Wasu 'yan kasar Chadi dauke da tutar kasar ta Chadi

Rahotanni na cewa wata tawaga ce da shi Adoum yake cikinta ta dauki hanyar zuwa garin Moundou domin kai ziyara ga Laokein Medar wanda ya yi takarar neman shugabancin kasar ta Chadi a shekara ta 2016 wanda kuma ake tsare da shi bisa zargin almundahana. Tun a ranar Asabar jami'an tsaro suka kama dan adawar.

Ministan cikin gidan kasar ta Chadi Ahmat Mahamat Bachir ya tabbatar da kamun da aka yi wa dan adawar, inda ya ce za a saurare shi kafin daga bisani a mika shi ga hannun shari'a. Wata sanarwa ta kungiyar kare hakin dan Adam ta Chadi wato CTDDH da ta yi Allah wadai da kamun, ta ce jami'an tsaron sun tsare tawagar ne sai kawai suka soma bincike daga bisani suka fito da wani gurneti, inda suka ce daga cikin motar dan adawar suka same shi. Sai dai kuma kungiyar ta nuna konkonto kan wannan zagi.