Chadi: An samu asarar rayuka a arangama tsakani makiyaya da manoma | Labarai | DW | 28.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi: An samu asarar rayuka a arangama tsakani makiyaya da manoma

Wani rikici tsakanin makiyaya da manoma a lardin Moyen-Chari da ke kudancin kasar Chadi ya yi sanadin rasa rayukan mutane 11.

Shugaban Chadi Idriss Deby

Shugaban Chadi Idriss Deby

Rahotanni sun ce mutane 11 aka kashe a wani tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma sakamakon wata takaddama dangane da lalata gonaki a kudancin kasar Chadi.

Gwamnan lardin Moyen-Chari Abbadi Sahir ya fada wa kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP cewa rikicin ya barke ne a ranar Litinin a gundumar Koumogo, abin da ya janyo asarar rayukan makiyaya uku da manoma takwas.

Rikici tsakanin manoma da Larabawa makiyaya na zama babbar matsala a yankin Sahel mai fama da kamfar ruwa, inda ake yawaita samun tashe-tashen hankula kan mallakar filin noma ko na kiwo.

Wani basaraken yankin da ya ce a sakaya sunansa ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarun na AFP yawan mutane da aka kashe, inda ya ce an kashe wani makiyayi ne bayan da shanunsa suka lalata shuki a wata gona. Su kuma makiyaya suka dauki fansa a kan manoman.