Fadan manoma da makiyaya ya hallaka jama'a a kasar Chadi
August 9, 2019Talla
Da yake magana da manema labarai a birnin N'Djamena, Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya bayyana rikicin kabilanci da na manoma da makiyaya da zaman wani babban bala'in da ke addabar kasar a yanzu, inda ya ci gaba da cewa masu rikicin sun yi ta bude wuta ga jami'an tsaron da aka tura a lardin don kwantar da tarzoma a lardin Ouaddai da ke gabashin kasar Chadi.