Cece-kuce kan ziyarar Netanjahu a Amirka | Labarai | DW | 02.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cece-kuce kan ziyarar Netanjahu a Amirka

Amirka na cigaba da nuna rashin jin dadinta dangane da wani jawabi da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai yi a zauren majalisar wakilan Amirka.

Jawabin na Mr. Netanyahu zai mayar da hankalinsa ne kan rashin amincewar da Isra'ila ta ke yi da shirin nukiliyar Iran da ma yiwuwar cimma matsaya a kan shirin tsakanin Iran din da Amirka, inda ya ke cewar bin hanyar laluma ba lallai ta kai ga cimma matsaya mai kyau ba.

Jam'iyyar Democrat ta Shugaba Barack Obama da ke mulkin Amirka da din da masu adawa da wannan ziyarar ta firaministan Isra'ilan na cewar wannan batu katsalandan ne ga harkokin siyasar Amirkan.

Da maraicen jiya Lahadi ne dai Mr. Netanyahu ya isa birnin Washington karkashin tsauraran matakan tsaro daidai lokacin da tsamin dangantaka ke cigaba wanzuwa tsakaninsa shugaba Obama.