1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cafke wani jigo a ƙungiyar Boko Haram

January 14, 2013

Rundunar JTF ta ce ta yi nasara cafke Mohammed Zangina ɗaya daga cikin masu faɗa a ji na ƙungiyar Boko Haram

https://p.dw.com/p/17JVq
A picture taken on April 18, 2011 shows Nigerian police enforcing a curfew in the capital of Bauchi state, nothern Nigeria, after riots, run by muslim youth, broke out in Bauchi. Nigeria's Goodluck Jonathan has been declared winner of presidential elections in a landmark vote that exposed regional tensions and led to deadly rioting in the mainly Muslim north. Jonathan, the incumbent and first president from the southern oil-producing Niger Delta region, won 57 percent of the vote in Africa's most populous nation, easily beating his northern rival, ex-military ruler Muhammadu Buhari. AFP PHOTO / Tony KARUMBA (Photo credit should read TONY KARUMBA/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images/AFP

Rundunar tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar Borno wacce aka fi sani da suna JTF ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke wani babban kwamandan ƙungiyar Boko Haram mai suna Mohammed Zangina da aka fi sani da Mallam Abdullahi Alhaji Musa wanda a kansa rundunar ta sa kuɗi Naira Miliyan 25 ga wanda ya kawo shi da rai ko a mace.

A cewar runudanar tabbatar da tsaro ta JTF Mohammed Zangina da aka fi sani da Mallam Abdullahi ko Alhaji Musa ɗaya daga cikin manyan ‘Yan Majalisar ƙoli da ake kira “Shura” ta ƙungiyar gwagwarmayar ne kuma yana da hannu a shirya yawancin hare-hare da aka kai a sassan ƙasar wanda ƙungiyar ta ɗauki alhakin kaiwa.

Kakakin rundunar Laftanar Kanar Sagir Musa ya bayyana cewa sun samu nasarar kama shi ne a Maiduguri bayan musayar wuta da aka yi, inda ya ƙara da cewa a baya ya sha tsallake kwanton ɓauna da aka yi a maɓoyarsa a garuruwan Jos da Zariya da Potiskum da Damaturu.

Kame wannan kwamandan na zuwa awowi 24 bayan da jami'an tsaron suka bayyana kame wani kwamandan ƙungiyar ta Ahlul Sunnan Li'dda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram a gidan wani tsohon ɗan majalisa wakilai da ya fito da jihar Borno.

Polizeiposten und gesperrte Straßen prägen den Alltag in der Millionenstadt Kano. Copyright: Katrin Gänsler Kano, Nigeria, 06.02.2012
Hoto: Katrin Gänsler

Sai jama'a na bayyana shakku kan wannan kame da jami'an tsaro suka ce sun yi na kuma tambayi Isma'il Yunusa wanda aka fi sani da malam Kaka ɗaya daga cikin masu wannan shakku inda ya bani dalilin sa kamar haka.

A baya ma dai rundunar ta annaya kame wasu manyan kwamnadojin yaƙi na wannan ƙungiya amma har yanzu ba kai ga bayyana su gaban al'umma ba wannan a cewar Malam Ahmad Gombe da lauje cikin naɗi in bah aka ba da an bayyana su.

Wata sabuwa kuma Rundunar tabbatar da tsaro da wanzar da zaman lafiya a jihar Borno ta sake jaddada cewa ɓoye ‘yan ƙungiyar Boko Haram da al'ummar jihar Borno ke yi da kuma rashin baiwa jami'an tsaro haɗin kai shine ke zama babban ƙalubale ga ƙoƙarin shawo kan matsalar rikicin.

Kakakin rundunar Laftanar Kanar Sagir Musa wanda ya bayyana hakan yace ya zama dole al'umma su taimakawa jami'an tsaron in dai ana son kawo ƙarshen wannan tashin-tashina.

Saboda haka ya shawarci al'ummar jihar da su fito su bayyana inda masu kai hare-haren ta hanyar baiwa jami'an tsaro haɗin kai da bayanai da zasu taimaka musu a ayyukan su.

Vor den Polizeiposten in Nordnigeria bilden sich oft kilometerlange Autoschlangen. Copyright: Katrin Gänsler Kano, Nigeria, 06.02.2012
Hoto: Katrin Gänsler

Sai dai da wuya jama'a su bada haɗin kai ga jami'an bisa hujjojin da al'umma ke bayarwa na rashin kyayyawan dangantaka tsakanin al'umma da jami'an tsaro kamar yadda malam Kaka da Ahmadu Gombe suka bayyana min.

To amma jami'an tsaron na musanta wannan zargi da al'umma ke yi inda suke kara karfafa guiwar su tare da daba tabbacin rufe asirin duk wanda ya taimaka musu.

Mawallafi:Al-Amin Mohammed Suleiman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi