Bush ya mayar da martani akan Iraki | Labarai | DW | 14.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush ya mayar da martani akan Iraki

Shugaba George W Bush ya mayar da martani adangane da sukan sabbin manufofinsa akan Iraki na kawo karshen tashe tashen hankula a wannan kasa,wanda ya gabatar a ranar larabar data gabata.A jawabinsa na mako mako ta gidajen Radio ,shugaba Bush yace wadannan manufofi nasa nada nufin karfafawa gwamnatin Iraki Gwiwa na daukan nauyin samar da tsaro a wannan kasa ,tare da bude babin sasanta kann kasar a siyasance.A ranar larabar data gabata nedai shugaban na Amurka ya sanar da tura karin dakarun soji dubu 21 zuwa kasar ta Iraki,sai dai kawo yanzu yan majalisar dokokin jammiyar Democrats masu rinjaye,na kokarin cimma kudurin dakatar da wannan yunkuri,idan har suka samu goyon bayan yan majalisar Repuclikan,ta hanyar mayar da Bush saniyar ware akan wannan batu.