Bush ya karbi rahoton nazari kan Iraki | Labarai | DW | 06.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush ya karbi rahoton nazari kan Iraki

Shugaba George W Bush na Amurka ya lashi takobin daukan matakan gaggawa adangane da shawarwarin da hukumar binciken halin da Iraki ke ciki ta gabatar masa,adangane da bukatar sauya manufofin sa a wannan kasa.Dayake karban rahotan hukumar da ke karkashin jagorancin tsohon sakataren harkokin wajen Amurka James Baker , mai jerin shawawari guda 79 ,shugaba Bush yace rahotan yayi nazari mai zurfi adangane da halin da kasar Iraki take ciki.

Hukumar kazalika ta jaddada cewa Amurka bazata cimma wata manufa na samar da zaman lafiya a Iraki,ba tare warware rigingimun dake tsakanin Izraela da larabawan palasdinu.