BUSH DA NUFINSA NA KOFAR DA SADAM YA JIMA | Siyasa | DW | 12.01.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

BUSH DA NUFINSA NA KOFAR DA SADAM YA JIMA

Tsohon sakataren maaji na shugaban Amurka George W Bush ya bayyana cewa tun kafin 11 ga watan satumban 2001 ayayinda a hannu guda kuma babban Limamin yan shiyya na kasar Iraki ya dada jada dadda matsayinshi na nuna adawa da shirin da Amurkan keyi na kafa gwamnati a wannan kasa.
Wannan bayanai na Poul O;Neil,ya samu goyon baya daga kwararru da masana dangane da cewa shugaban na Amurka a lokaci mai tsawo daya gabata yasha muradin ghanin bayan gwarzon namiji kuma shugaban na Iraki Sadam Hussein,wanda yaasha kushe Amurka da manufofinta na kasancewa yar sandar Duniya. Sakataren Maajin ya fadawa gidan Talabijin din CBS a hirar da akayi dashi jiya Lahadi cewa,tun daga far shugaba Bush ya bayyana Sadam da kasasncewa mutum mai munanan Akida,kuma dole ne a kifar da gwamnatinsa.
A halin yanzu da ake cigaba da shirye shiryen zabe a kasar ta Iraki,wanda kuma wasu shugabannin kasar ke adawa da shi,kalaman na O;Neill a jiya ya fara daukan hankalin jamaa,kafin a wallafa Littafi daya rubuta mai suna The Price of Loyalty.
Ya fadawa Time magazine cewa a kasancewa da yayi na tsawon watanni 23 a wannan wuri,bai taba gani ko kuma jin wata shaida a dangane da cewa akwai makaman kare dangi a Iraki ba. Shugaba Bush ya haye ragamar mulkin Amurka a watan janairun shekarata 2001,kuma acikin watanni ukunsa na farko ,jamian kasar suka fara laakari da yadda zasu iya kifar da Sadan daga shugabancin Iraki,da kuma shirin yadda kasar zata kasance bayan yaki,kamar yadda wasu takardu da sukafito daga wasu jamian fadar gwamnati suka mikawa mawallafin takardan Ron Suskind.
O,Neill ya fadawa Suskind cewa yayi mamakin,daga cikin masu bawa shugaba Bush shawarwari kann harkokin tsaro ,babu wanda ya tambayeshi dalilansa na afkawa Iraki da yaki.A watan Disamban shekara ta 2002 ne shugaba Bush ya kari O;Neill daga mukaminsa.
A hannu guda kuma kuma Prime ministan Britania Tony Blair wanda yasha bayyana cewa zaa gano makaman Nuclear a Iraki,a jiya Lahadi yace ba lalle bane a gano wadannan makaman.
Abunda keda muhimmanci a halin yanzu shine jamaa sun tabbatar dacewa shugaban na Amurka na sane dacewa Iraki bata mallaki wadannan makamai na kare dangi ba,dalili kenan dayasa Amurkan ta jagoranci afka mata da karfin sojin tunda Bush tuni ya lashi takobin ganin bayan Sadam Hussein.Inda yayi amfani da bayanann karya wajen samun goyon bayan duniya kann cewa iraki nada makama masu guba ,wanda kuma na iya kasancewa barazanace.
 • Kwanan wata 12.01.2004
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvme
 • Kwanan wata 12.01.2004
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvme