Burundi zata samu taimakon dala miliyan 170 | Labarai | DW | 01.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burundi zata samu taimakon dala miliyan 170

Masu bada gudumowa na kasa da kasa sun amince baiwa gwamnatin kasar Burunsi taimakon dala miliyan 170 cikin wannan shekara,domin taimaka mata biyan bukatunta na gaugawa sakamakon fari da yaki da suka tagaiyara kasar.

Mataimakiyar shugaban kasa ta 2,Alice Nzomukunda ta fadawa manema labarai a karshen taron kasashe masu bada gudumowa cewa,kasashe da hukumomi da ke kan gaba wajen bada wannan gudumowa sun hada da,babban bankin duniya,Burtaniya Amurka,Netherlands Faransa da Switzerland.

Kasar ta Burundi dai ta bukaci taimakon dala miliyan 168 don taimakawa jamaarta da fari ya shafa,gina makarantu da inganta harakar kula da lafiya.

Kamar sauran kasashe makwabta kasar Burundi tana fama da karancin abinci saboda fari daya abka masu.

Kasar Burtaniya ta alkawarta bada fam miliyan 9.

Mahukuntan Burundi sunce mutane akalla 200 ne suka rasa rayukansu sakamakon yunwa tun watan disamba,dubbai kuma sun tsere zuwa wasu kasashe domin gujewa yunwa.

Yanzu haka dai kungiyoyin kare hakkin bil adama,sun bukaci masu bada gudumowar dasu matsawa gwamnatin Burundi lamba ta kawo karshen azabtarwa tare da kisan wadanda take zargi da alaka da kungiyar yan tawaye ta FNL,wacce ita kanta take kai hare hare kan farar hula.