Burundi ta shirya ma zaben 'yan majalisa
June 28, 2015Hukumar zaben kasar Burundi ta ce ta shirya wa zaben gobe Litinin, duk da tashe-tashen hankula da ake fuskanta masu nasaba da zaben. Mutane biyu sun hallaka a birnin Bujumbura fadar gwamnati kwana daya kafin zaben. Shugaban hukumar zaben ya ce tuni aka rarraba kayayyakin zabe a cikin mazabu fiye da 11,000 saboda zaben na 'yan majalisar dokokin.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya na cikin wadanda suka nemi a jinkirta zaben, yayin da 'yan adawa suka janye, saboda shirin Shugaba Pierre Nkurunziza na sake takara domin neman wa'adi na uku. Fiye da mutane 70 suka hallaka cikin tashe-tashen hankulan na kasar ta Burundi, sannan manyan jami'ai na hukumar zabe, da fannin shari'a gami da mataimakin shugaban kasa na cikin dubban mutanen da suka arce daga kasar mai fuskuntar yiwuwar yakin basasa.