Burundi ta kori ′yan Belgium | Labarai | DW | 20.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burundi ta kori 'yan Belgium

Jam'iyya da ke mulki a Burundi ta bukaci 'yan kasar Belgiyum da su fice daga kasar bayan da suka zarge su da hada kai da 'yan adawa wajen rura wutar rikicin siyasa a kasar.

Jam'iyyar ta CNDD-FDD ta Shugaba Pierre Nkurunziza ta kuma ce 'yan kasar ta Belgiyum da ke zaune a Burundin na yunkuri ne wajen ganin an kawar da gwamnati mai ci daga gadon mulki.

To sai dai tuni 'yan Belgiyum din suka musanta wannan zargi. Gabannin wannan dai, a makon jiya gwmanatin Belgiyum ta shawarci 'yan kasarta da su fice daga Burundin din duba da yadda lamura ke ciga da dagulewa a kasar.