1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahara sun kashe mutane 26 a Burundi

Ahmed Salisu
May 12, 2018

Rahotanni daga kasar Burundi na cewar wasu 'yan ta'ada sun hallaka mutanen da yawansu ya kai 26 a wani kauye da ke yankin arewa maso yammacin kasar a wannan Asabar.

https://p.dw.com/p/2xaGp
Burundi Gewalt und Tote
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Ministan kula da harkokin tsaro na al'umma a kasar Alain Guillaume shi ne ya bayyana hakan inda ya ke cewar maharan sun kuma jikkata mutane 8 kafin daga bisani su arce zuwa Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Tuni dai gwamnatin Kongo din ta yi Allah wadai da wannan hari na Ruhagarika inda ta ce ta tuntubi hukumomin Kongo din kan su yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin sun kame wanda ke da hannu kan wannan aika-aika da nufin ganin sun fuskanci hukunci.