Burundi: Kwalara ta hallaka mutane 30 | Labarai | DW | 22.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burundi: Kwalara ta hallaka mutane 30

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu matuka dangane barkewar cutuka ciki kuwa har da cutar nan ta amai da gudawa ko Kwalara a sansanin 'yan gudun hijirar 'yan Burundi.

Tansania Flüchtlinge aus Burundi

Dubban 'yan kasar Burundi ne ke gudun hijira a Tanzaniya

Cinkoson mutane da ake samu a wasu yankuna da ke wani kauye a Tanzaniya inda 'yan Burundin din ke samun mafaka da rashin tsabta gami da karanci matakai na kula da lafiya na daga cikin abubuwa da ake tunanin sun kai ga haifar da bullar cutuka.

Rahotanni dai na cewar ya zuwa yanzu an samu rasuwar mutanen kimanin 30 sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa, kuma ana zaton yawan wanda cutar ta hallaka ka iya karuwa.

Dubban 'yan Burundi din ne dai ke samun mafaka a kasar ta Tanzaniya sakamakon tada zaune tsaye da aka samu a kasar biyo bayan rikicin siyasa da ta shiga sanadiyyar yunkurin shugaban kasar Pierre Nkurunziza na yin tazarce.