Burkina: Sojin gwamnatin sun kwance damarar RSP | Labarai | DW | 30.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burkina: Sojin gwamnatin sun kwance damarar RSP

Bayaga kwance damarar rundunar RSP da aka yi an kuma kwace barikin Naaba Koom da ke a birnin Ouagadougou bayan musayar wuta ta wani lokaci.

A yammacin jiya Talata sojojin da ke biyayya ga gwamnatin rikon kwarya ta kasar sun yi nasarar karya lagon rundunar sojin RSP tare ma da kwace barikinta ta Naaba Koom da ke a birnin Ouagadougou bayan masayar wuta ta wani lokaci.

Sojojin rundunar ta RSP wacce ta kifar da gwamnatin rikon kwarya ta kasar yau da 'yan kwanaki kafin ta sake mika mulkin, a sakamakon matsin lambar kasashen duniya, sun ki amincewa da matakin kwance masu damara da gwamnatin ta dauka. Abin da ya kai sojojin da ke biyayya ga gwamnatin yin amfani da karfin tuwo domin tilasta masu yin hankan.

Janar Pingrenoma Zagre babban hafsan sojojin kasar ta Burkina Faso, wanda ya jagoranci harin kwance damarar rundunar ta SRP ya ce a halin yanzu lamura sun daidaita komi ya dawo hannunsu. Sai dai jagoran juyin milkin da ya yi raggon kaya a kasar ta Burkina Janar Diendere ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, cewa yana fargabar an samu mutuwar mutane da dama.