1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana yin Allah wadai d juyin mulkin Burkina

Abdourahamane Hassane
January 25, 2022

kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso inda suka kifar da gwamnatin mulkin farar hula ta Roch Marc Christian Kaboré.

https://p.dw.com/p/464Zw
Burkina Faso Anhänger feiern Militärputsch
Hoto: OLYMPIA DE MAISMONT/AFP

Babban sakataran MDD Antonio Guterres, ya ce ba za su taba amincewa ba da juyin mulkin sojoji ba a yammacin Afirka wanda ya yi kira ga sojoji da su kare kasashensu daga 'yan ta'adda a maimakon kodayen kwatar mulki.Tun farko kungiyar ECOWAS da kungiyar tarayar Afirka sun yi Allah wadai da juyin mulkin. Dubban jama'a a Burkina Faso sun gudanar da gamgami na nuna goyon baya ga sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hular.