Burkina gwamnati ta ja hankali ′yan adawa | Labarai | DW | 25.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burkina gwamnati ta ja hankali 'yan adawa

Hukumomi a Burkina Faso sun yi kashedi ga duk wanda zai iya kawo yamutsi a cikin kasar daidai lokacin da ake dakon hukumar zabe ta bayyana sakamakon zaben kasar.

Burkina Faso Wahlen 2020 | Zephirin Diabre

Zéphirin Diabré jagoran 'yan adawa

Hakan kuwa ya biyo bayan sanarwar da 'yan adawar kasar suka bayyana na cewar an tafka magudi a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin da aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata wanda suka yi brazanar cewar ba za su amince ba da sakamakon zaben. A cikin wata sanarwa da minista yada labarai na Burkina Fason Remi Fulgance ya bayyana ya ce gwamnati ba za  taba amincewa ba da tada zauna tsaye.