1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe a kasar Burkina Faso

Zainab Mohammed Abubakar
November 21, 2020

A wannan Lahadin ake gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisa a Burkina Faso. Sai dai barazanar harin 'yan ta'adda na iya hana al'ummar kasar fita wajen kada kuri'u.

https://p.dw.com/p/3leV2
Burkina Faso | Übung Truppen aus Afrika
Hoto: picture-alliance/Zuma/Planet Pix/D. White

A kowace rana dai matsalar tsaro sai kara tabarbarewa take. Sore Ouesseni mazaunin unguwar Quidi da ke babban birnin kasar watau Ouagadougou, da maraice sukan zauna da abokansa ana hira irin ta majalisa a kofar shagonsa.

Ouesseni na sayer da kayan safiyo na gyaran bandaki da kayan tsabtace gida. Sai dai a 'yan kwanakin sun yi wuyar gani, saboda an lullube kantin nasa da postan hotunan shugaba Roch Kabore da jam'iyyarsa ta MPP. An fenta komai a launin lemo, wada ke wakiltar launin jam'iyyar da ke mulkin.

Ouesseni na da yakinin cewar mafi yawa daga cikin al'ummar kasar ta Burkina Faso zasu kada kuri'unsu domin sake zabar shugaba Kabore mai shekaru 63 da haihuwa, wanda ke neman wa'adin shekaru biyar a karo na biyu a zaben na yau.

" A wannan rana ta 22 ga watan Nuwamba, zamu fito kwanmu da kwartarmu domin zaben shugaba Roch Christian Kabore. Wajibi ne ya lashe wannan zabe. Saboda mutumin kirki ne, yana aiki sosai. Bashi da wata matsala, mutum ne mai kaunar aiki".

Kabore ya dare karagar mulki ne bayan boren adawar shekara ta 2014 da ya kifar da gwamnatin tsohon shugaba Blaise Compaore, wanda mulki Burkina Faso na tsawon shekaru 27.

Burkina Faso Präsident Roch Marc Christian Kabore
Hoto: Ludovic Marin/Pool/abaca/picture alliance

Sai dai babu kade kaden da aka saba yi a gaban babban ofishin jam'iyyar da ke mulki ta MPP. Kazalika babu tawagar masu rawar gargajiya da kan kan hadu domin yin bukukuwan nuna goyon baya ga dan takararsu.

Ana iya ganin daidaikun mutane sanye da kaya masu lauyin jam'iyyar ta Kabore, sai dai baka iya tantance magoya bayan sauran 'yan takara 12 da ke fafatawa da shi a zaben na wannan Lahadi.

Manyan masu kalubalantar Kabore dai su ne dan takarar jam'iyyar UPC Zephirin Diabre mai shekaru 61 da kuma Eddie Komboigo dan takarar jam'iyyar CDP ta tsohon shugaba Compaore.

Bincike na nuni da cewar wadannan 'yan takara biyu na iya samun kaso 10 zuwa 11 daga cikin 100 na yawan kuri'u da za a kada. Sandrine Nama ita ce shugabar tuntuba ta kungiyar tattauna lamuran tsaro mai zaman kanta mai suna Burkinabe..

"Yawancin 'yan takarar na muradin tattaunawa da 'yan ta'adda. A garesu wannan ne tubalin gano bakin zaren rikicin kasar. A gaskiya wannan rikici ya ritsa da iyalai da dama. Don haka wajibi ne a samo mafita cikin gaggawa ta ayi gwada duk damarmakin da ke da akwai".

Symbolbild Wahlen in Burkina Faso
Hoto: Olympia de Maismont/AA/picture alliance

Matsalar tsaron da ke addabar yakin Sahel dai sannu a hankali na shiga Burkina Faso. Kungiyoyin 'yan ta'adda masu yawa da ke kai hari a Mali  da ke makwabtaka sun sha kaddamar da hare hare a cikin kasar a 'yan shekarun da suka gabata.

Gwamnatin tsohon shugaba Compaore dai na da alakar kut da kuta da shugabannin wadannan kungiyoyin tarzoma da ke  kai hari a wajen kasar. Tun bayan kifar da mulkinsa ne kuma hare hare suka tsanata acikin Burna Faso.

An kiyasa cewar  mutane 2,730 suka rasa rayukansu cikin tsukin watanni 12 da suka gabata daga rikicin cikin gida dana 'yan ta'adda.Abun da am'ummar Burkinan ke muradi daga kowane shugaban da zai ci zaben na yau shi ne, zaman lafiya.