1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso za ta dauki sabbin dakarun soji

February 24, 2023

Burkina Faso na shirin daukar sabbin jami'an soji kimanin dubu biyar da za su yi aiki a rundunar sojin kasar na tsawon shekaru biyar domin yaki da ta'addanci a kasar.

https://p.dw.com/p/4NvQZ
Dakarun sojin Burkina Faso a birnin Ouagadoudou
Hoto: Kilaye Bationo/AP Photo/picture alliance

A cikin sanarwar da ministan tsaron kasar kanal Kassoum Coulibaly ya fitar, ya ce za a dauki sabbin dakarun da ba su aiki a yanzu ne daga sassa daban-daban na kasar. Ya kara da cewa za a ci-gaba da daukar matasan sojojin ne daga ranar 28 ga watan Fabarairun zuwa 7 ga watan Maris din wannan shekarar, wadanda aka haife su tsakanin shekarar 1988 zuwa shekarar 2003.

Wannan dai shi ne karo na uku cikin tsukin shekara guda da rundunar sojin ta dauki sabbin jami'ai. Kasar Burkina Faso ta shafe shekaru ta na fama da matsalar tsaro wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu 1 yayin da wasu miliyan 2 suka rasa matsugunansu.