Burkina Faso: Za a fara binciken gawa | Labarai | DW | 16.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burkina Faso: Za a fara binciken gawa

Masu gabatar kara a Burkina Faso sun kaddamar da bincike mai tsanani kan mutuwar wasu mutane 11 a ofishin hukumar yaki da sha da fataucin kwaya a babban birnin kasar Ouagadougou.

Mai gabatar da kara a kasar Maiza Sereme ta ce an bude babin binciken ne da neman kwararru su gudanar da sahihin bincike kan gawarwakin don tabbatar da silar mutuwarsu. An tsare mutanen ne bayan kamasu da zargin ta'ammali da muggan kwayoyin da ke sa maye.

Matsalar muggan kwayoyi na cikin manyan matsalolin kasar Burkina Faso, inda ake ganin rashin aiki ya sa kasar zama daya a cikin cibiyoyin kwayoyi a yammacin Afirka domin safararsu zuwa arewacin Mali da Libiya.