1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mahaka zinare a Burkina Faso

Gazali Abdou Tasawa
October 6, 2019

A Burkina Faso mutane kimanin 20 sun halaka yayin harin da wasu 'yan bindiga suka kai a wata mahakar zinare ta gargajiya a kauyen Dolmane da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/3QmxS

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito wasu majiyoyin tsaro na kasar ta Burkina Faso na cewa maharan dauke da bindigogi sun kai harin ne a yamamcin ranar Juma'ar da ta gabata, inda suka bude wuta kan mahaka zinaren tare da halaka 20 kana wasau da dama suka jikkata.

 A wannan yanki ne dama a tsakiyar watan Satumban da ya gabata, mayakan kungiyoyin da ke da'awar jihadi suka tarwatsa wata gada da ke kan hanyar biranen Djibo da Dori na arewacin kasar. A ranar Litinin din makon da ya gabata ma dai fararen hula tara ne suka halaka a cikin wasu jerin hare-hare da aka kai a garuruwan Pissele da Boulkiba na karamar hukumar Bourzanga ta jihar Bam a arewacin kasar, kana wasu mutane sama da 20 suka mutu a wasu jerin hare-haren a jihar ta Bam, lamarin da ya tilasta wa mutane sama da dubu 20 tserewa zuwa birnin Kongoussi.